The Hidden Geometry of Folio 86v: The T-Axis and Code 4
#8
Bincikena ya nuna mini cewa wannan littafi na Voynich ba abu daya yake magana a kai ba taska ce da ta tattara fannoni da dama na ilimi. Kuskuren da mutane da yawa suke yi shi ne kokarin hada ma'anar shafi daya da wani alhalin kowane sashe yana da nasa dokokin da mabudin fahimta.
Misali idan marubucin yana magana kan ilimin magunguna yana iyakance bayaninsa a wadancan shafukan ne kawai. Idan mutum bai fuskanci shafin baya ya fahimci inda magana ta tsaya ba to ba zai taba fahimtar inda shafi na gaba ya dosa ba. Ma'ana takan rikice ne idan aka dauko dokar sashen taurari aka so a yi amfani da ita a sashen taswira.
Don haka kafin mu ci gaba da nazarin taswirar Rosettes dole ne mu yarda cewa littafin nan gundumomi ne (sections) kuma kowane sashe rufaffen babine na kansa kafin a bude wani sabon ilimin.
this is my own logic about the book. i think the book is many sections. you cant mix herbal page with map page. if you dont understand the page before you will be lost in the next page. this is why people get confuse. i study it section by section. please translate my hausa to understand my method.

Surayya munir isah
Bahaushiya daga nigeria
Reply


Messages In This Thread
RE: The Hidden Geometry of Folio 86v: The T-Axis and Code 4 - by Surayya munir isah - 18-02-2026, 05:17 AM

Forum Jump:


Users browsing this thread: